Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya sanar a yau Laraba cewa, bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi masa, ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Saliyo Samura Kamara zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 13 zuwa 16 ga watan nan da muke ciki.(Lami)