Kamara ya bayyana cewa, Saliyo na goyon bayan kasar Sin kan wannan batu, tana kuma fatan bangarorin masu ruwa da tsaki za su girmama juna, tare da neman hanyar warware batun cikin lumana. Kana ya yi kira ga kasashen duniya, da hukumomin dake da hannu wajen yanke hukunci kan batun, za su taka rawar da ta dace, ta hanyar tabbatar da zaman lafiya da lumana a yankin tekun kudancin kasar Sin.
Bisa gayyatar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, Kamara zai kawo ziyara nan kasar Sin tsakanin ranekun 13 zuwa 16 ga wannan wata.
Mr. Kamara ya ce, wannan ziyara ta sa, ta biyo bayan ziyarar Wang Yi a kasar Saliyo a watan Agustar bara. Kuma nan gaba, bangarorin biyu za su kara fadada mu'amala da juna, kan ayyukan da suka cimma shawarwari a kan su. (Zainab)