in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta baiwa Liberia taimakon kayayyakin soja
2016-02-11 12:20:27 cri
Shugabar kasar Liberiya Madam Ellien Johnson Sirleaf ta yabawa mahukuntan kasar Sin bisa taimakon kayayyakin da ta baiwa rundunar sojan kasar.

Shugaba Sirleaf wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ce kayayyakin da aka kiyasce kudinsu zuwa dala miliyan uku, sun zo a dai-dai lokacin da galibin kayayyakin da sojojin kasar suke amfani da su suka lalace.

A jawabinsa jakadan kasar Sin da ke Liberiya Zhang Yue ya yaba da irin nasarorin da shugaba Sirleaf ta cimma a fannin tattalin arziki da samar da kayayyakin more rayuwa. Yana mai cewa, tallafin kayayyakin, wata alama ce da ke kara nuna imanin kasar Sin da kuma goyon bayan kokarin kasar Liberiya na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, a yayin da tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar (UNMIL) ke gudanar da aikinta da kuma jadawalin farfado da kasar bayan barkewar cutar Ebola. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China