in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liberia za ta kasance kasa ta baya bayan nan a Afirka da ta shiga WTO
2015-10-19 11:01:22 cri
Bisa labarin da aka bayar a shafin intanet na ma'aikatar cinikayya da masana'antu ta kasar Liberia, ya nuna cewar kasar ta gabatar da aniyar ta na shiga kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, wannan ya bayyana cewa, an kammala daukar matakai na karshe don shigar da Liberia kungiyar WTO.

Ana sa ran gabatar da kuduri a gun taron ministoci karo na 10 na kungiyar WTO da za a gudanar a birnin Nairobi na kasar Kenya a watan Disambar bana. Idan kasar Liberia ta cimma nasarar shiga WTO, za ta kasance kasa ta karshe a nahiyar Afirka da ta shiga WTO.

Kasar Liberia tana yammacin nahiyar Afirka, kuma tana daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya. An fara yin shawarwari kan shigar da kasar Liberia a kungiyar WTO ne a shekarar 2007. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China