Kasar Rasha ta tsawaita wa'adin takunkumin da ta saka wa kasashen yammacin duniya
A jiya ne shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya sa hannu kan wani umarnin da ya bayar, inda ya tsawaita wa'adin takunkumin da kasar ta kakabawa kasashen yammacin duniya, daga ranar 6 ga watan Augustan shekarar 2016, karshen wa'adin da aka tanada a baya, zuwa karshen shekarar 2017.
Bayan barkewar rikici a kasar Ukraine ne, kasar Amurka da kasashen kungiyar tarayyar Turai EU suka fara sanyawa kasar Rasha takunkumi, abin da ya sanya shi ma shugaba Putin na kasar Rasha ya ba da umarnin hana shigowa da kayayyakin amfani gona, da abinci daga kasashen da suka kakabawa kasarsa takunkumi.(Bello Wang)