in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari tsakanin Abbas da Ban Ki-Moon
2016-06-29 11:15:00 cri
Jiya Talata, shugaban Falestinawa Mahmoud Abbas ya yi shawarwari tare da babban sakataren MDD Ban Ki-Moon, wanda ke ziyara a kasar, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan da suka shafi shawarar Faransa, da sake raya Gaza, da kuma neman jituwa a Falestinu da dai sauransu.

A yayin taron manema labaru da suka shirya bayan shawarwarin, mista Abbas ya bayyana cewa, bangaren Falestinu har yanzu yana kan alkawarin da ya dauka game da shirin na kasashen biyu, yana kuma fatan tabbatar da zaman lafiya a shiyyar ta hanyar yin shawarwari. Amma, a waje guda ya nuna cewa, matakin da kasar Isra'ila ta dauka, da ci gaba da mamaye da fadada matsugunan Yahudawa sun lahanta shirin kasashen biyu, kuma ba su da amfani ga zaman lafiyar yankunan.

Ba ya ga haka, Abbas ya nuna yabo ga kokarin da kasashen duniya ke yi na inganta taron zaman lafiya na duniya, ya kuma jaddada muhimmancin shawarar Faransa. Bisa shawarar da Faransa ta gabatar, an yi hasashen cewa, za a kira taron zaman lafiya na duniya, da nufin warware matsala a tsakanin Falestinu da Isra'ila a karshen shekarar bana, inda za a bullo da wani tsari da zai tabbatar da wannan batu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China