Rundunar Congo ta samu goyon bayan dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dake kasar (MONUSCO), kana kuma ayyukan da aka kaddamar tun cikin watan da ya gabata kan mayakan ADF, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane dubbai a yankin Beni dake arewacin Kivu.
A gundumar Ituri, mayakan sa kai na kungiyar 'yan tawayen Ituri (FRPI) guda 10 aka kashe a yayin wani gumurzu tsakanin rundunar sojojin FARDC da mayakan a kauyen Kienge na masarautar Walendu Bindi a ranar Litinin da ta gabata.
A cewar majiyoyin soja, gumurzun ya barke a lokacin da sojojin FARDC suka fara ayyukan zakulo sansanonin mayakan sa kai dake kokarin sake hadewa tun fiye da mako guda da ya gabata a wannan yanki na gundumar Ituri.
A cikin wata sanarwa, komandan na biyu na bangaren FARDC dake Ituri ya bayyana cewa wadannan 'yan tawaye na yunkurin sake hadewa domin yawaita hare-harensu kan fararen hula. (Maman Ada)