in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Senegal ya gana da memban majalisar gudanarwar kasar Sin
2016-05-07 12:55:09 cri

A jiya Juma'a, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya gana da memba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi a birnin Dakar.

Yang Jiechi ya isar da sakon shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaban na Senegal.

Yang Jiechi ya bayyana cewa, burin ziyararsa a wannan karo shi ne aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma a wajen taron koli na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a birnin Johannesburg, da kara yin hadin gwiwa kan manufofin bunkasa kasashen biyu, da sa kaimi ga sada zumunta da samun moriyar juna a tsakaninsu.

Sall ya bayyana cewa, taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Jahannesburg ya taimaka wajen raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Jawabin shugaba Xi Jinping ya dace da bukatun bunkasuwar kasashen Afirka, wanda ya samu karbuwa a tsakanin jama'ar kasashen Afirka. Ana raya dangantakar dake tsakanin Senegal da Sin, da samun sakamako kan hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, kana bangarorin biyu sun cimma daidaito kan manyan batutuwa. Kasar Senegal ta nuna godiya ga kasar Sin domin ta samar da gudummawa ga Senegal wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

A wannan rana kuma, Yang Jiechi ya yi shawarwari tare da firaministan kasar Senegal Mahammed Dionne, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China