in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu na shirin mayar da yara miliyan guda makaranta
2016-05-09 11:10:31 cri
Sabon ministan ilimi a gwamnatin hadin kan kasar Sudan ta kudu Deng Deng Hoc, ya ce ma'aikatar sa na da burin mayar da yara kanana da yawan su ya haura miliyan guda zuwa makaranta.

Mr. Hoc, wanda ya zanta da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya ce nan gaba kadan, yaran da tashe tashen hankula na kabilanci suka raba da makarantu, za su samun damar komawa azuzuwa domin fara darussa.

Ya ce muhimmin aikin da za su sanya gaba shi ne kara gina makarantu, da daukar sabbi, tare da horas da malaman makaranta, kasancewar yanzu haka bisa kiyasi, malami guda na kula da yara da yawan su ya kai 150.

A baya ma wakilin asusun yara na UNICEF a Sudan ta Kudun Jonathan Veitch, ya taba bayyana cewa Sudan ta kudun ce ke kan gaba a duk duniya, wajen yawan yara kanana da ba sa zuwa makaranta sakamakon yakin basasa da ya daidaita kasar.

A cewar sa akwai yara sama da miliyan daya da dubu dari 8, wato sama da rabin yaran kasar, wadanda ba su da damar zuwa makaranta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China