Babban akalin soja na Ouagadougou, kanar Norbert Koudougou ya bayyana cewa wadannan sammaci za a sake duba su sannan a sake nema, bayan matakin kotun daukaka kara.
Kotun soja ta Burkina Faso ta nemi sammacin mista Soro, kan hannunsa game da juyin mulki kan gwamnatin wucin gadi, a cikin watan Disamban shekarar 2015, yayin da shi kuma mista Campaore ake zarginsa da hannu kan kisan tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara.
Kotun daukaka kara ta Ouagadougou ta soke baya bayan nan wadannan sammcin biyu dalilin rashin karfaffar shaida.
Soke wadannan sammaci kan mutanen biyu, tare da wasu mutane goma ya janyo rashin fahimtar a cikin zukatan al'ummar Burkina Faso.
A cikin wata sanarwa, a ranar Jumma'a, gungun "Le Balai Citoyen" babban jagoran bore na karshen watan Oktoban shekarar 2014 a kasar Burkina Faso, yayi allawadai da wannan mataki, tare da yin kashedi ga hukumomi na yanzu tare da bayyana su a matsayin masu laifi kan duk wani tabarbarewar yanayi a Burkina Faso. (Maman Ada)