Da farko dai, kasar Sin ta dade tana da ikon mulki a yankin tekun kudancin Sin, har ma dukkan gwamnatocin kasar Sin na da da na yanzu sun tsaya tsayin daka kan wannan iko. Ana da isassun abubuwan shaida na tarihi na sahihanci game da wannan batu, kuma ba a bukatar tabbatar da wannan ta hanyar gina tsibirai ba.
Na biyu, bangaren Sin ya dauki matakan yin gine-gine a wasu tsibiran inda kasar Sin take da ikon mulkinsu kuma lamari ne da kasar Sin ta yi bisa doka, kuma hakan bai kawo kowace irin illa ga sauran kasashe ko kadan ba.
Na uku, ta kasance tamkar wata babbar kasa, kasar Sin na kokarin sauke nauyin kasa da kasa da aka dora mata. Bangaren Sin ya yi aikin yin gine-gine a wasu tsibirai ne domin kokarin sauke nauyin ceto a tekun, da kawar da bala'u daga indallahi, da aikin sa ido kan sauyin yanayin duniya, da kokarin kiyaye muhalli da kuma tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa kan teku da ayyukan kamun kifi a yankin tekun.
Na hudu, cikin dogon lokacin da suka gabata, kasa da kasa suna da 'yancin tafiyar da jiragen ruwa da jiragen sama cikin tekun kudancin kasar Sin, wannan ya dace da dokar duniya, amma bai kamata wasu kasashen duniya su keta dokar ba, balle ma kawo rauni ga mulkin kai da tsaron kasashen dake kewayen tekun kudancin kasar Sin.
Kana aikin kafa tsibiran da kasar Sin ta yi a tekun ba zai hana 'yancin kasa da kasa ba wajen shawagin jiragen sama da jiragen ruwa a tekun ba, kuma zai ba da taimako wajen fuskantar wasu kalubaloli cikin hadin gwiwa a kan teku, da kuma ba da tabbaci ga tsaron jiragen ruwa dake tafiya a kan tekun kudancin kasar Sin.
Na biyar, a halin yanzu, kasar Sin da kasashen kungiyar tarayyar kasashen Asiya ta kudu maso gabas ta ASEAN sun riga sun cimma ra'ayi daya kan warware batun tekun kudancin kasar Sin, watau, ya kamata a warware sabani dake tsakanin kasashen da abin ya shafa ta hanyar yin shawawari, ya kamata kasar Sin da kungiyar ASEAN su kiyaye zaman lafiya da zaman karko na tekun kudancin kasar Sin cikin hadin gwiwa. Kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN na ciyar da shawarwarin tsara ka'idojin batun tekun kudancin kasar Sin gaba, bisa sanarwar da bangarorin da batun tekun kudancin kasar Sin ya shafa suka fidda.
Kuma, tsara ka'idojin aiki ne dake tsakanin kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN, ya kamata kasashen su tsara da kansu, ana fatan kasashen Amurka da wasu kasashen wadanda ba su cikin yankin, su girmama kokakin da kasar Sin da kasashen ASEAN suka yi, bai kamata su haifar da karin matsaloli ga shawarwarin dake tskanin Sin da ASEAN kan batun.
Na shida, batun tekun kudancin kasar Sin ba shi da nasaba da kasar Amurka, don haka bai kamata ya kasance wata matsala a tsakanin kasashen Sin da Amurka ba. Da babbar murya kasar Sin ta kalubalanci Amurka ta yi hangen nesa bisa yadda ake raya dangantaka a tsakanin kasashen 2 da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta cika alkawarinta na rashin tsayawa a kan wani matsayi dangane da batun ikon mulkin kasa da yankunan kasa, wanda ake rigima kansu a kai, ta girmama kokarin da kasashen da ke yankin suke yi na kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun, ta yi taka-tsantsan, ta kuma daina yin bayani ko daukar mataki, wadanda za su lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin da kuma dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka. (Sanusi, Tasallah , Maryam)