A sakonsa na fatan alheri da taya murna ga taron,shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, game da makomar samun bunkasuwar Sin, kasarsa za ta martaba manufar kirkiro da sabbin abubuwa, da daidaita mabambanta yankunan, da kiyaye muhalli, da bude kofa ga kasashen waje, da cin gajiyar fasahohin da aka samu, kana za ta dauki jerin matakai, don raya makamashi masu tsabta, da kyautata tsarin sana'o'i da yin amfani da makamashin ba tare da gurbata muhalli ba, da yin gine-gine da raya harkokin zirga-zirga a kasa, tare da kiyaye muhalli.
Sin za ta yi kokarin kiyaye muhalli, don sa kaimi ga zaman jituwa tsakanin Dan Adam da muhallin halittu, in ji shugaban.
Shugaba Xi ya ce, a shekara mai zuwa, Sin za ta dauki bakuncin taron ministoci karo na 8 game da samar da makamashi masu tsabta, yana fatan wakilan kasashen duniya za su zo kasar Sin, don yin mu'amala da yada fasahohin da suka samu wajen yin amfani da makamashi masu tsabta, don ci gaba da ingiza samun dauwamammen ci gaba a doron kasa.(Bako)