A jawabinsa na fatan alheri, firaminista Li ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai game da harkokin yawon shakatawa, sannan ta fidda jerin dokoki da manufofi wajen sa kaimi ga yin gyare-gyare da raya sha'anin yawon shakatawa a kasar Sin. An dauki wannan matakin ne don mayar da sha'anin yawon shakatawa a matsayin wani ginshikin raya tattalin arzikin kasar bisa manyan tsare-tsare, ta yadda harkokin yawon shakatawa za su kara gamsar da jama'a yadda ya kamata.
Firaministan ya jaddada cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin Sin za ta yi amfani da sha'anin yawon shakatawa don rage yawan masu fama da talauci kimanin miliyan 12.
A karshe, ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta gabatar da shirin yin hadin gwiwa game da harkokin yawon shakatawa na duniya, don sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya, da yin amfani da wannan fanni don ya zama hanyar samun zaman lafiya, ta yadda hakan zai ba da gudummawa game da yin mu'amalar sada zumunta da zaman tare cikin jituwa, da bude kofa ga kasashen waje.(Bako)