Firaministan ya ce, Sin tana goyon bayan kokarin da kasar Mozambique ta ke yi wajen tabbatar da tsaro da sulhunta kabilun kasar, kuma Sin tana fatan taimakawa kasar Mozambique wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'ummominta. kasar Sin tana goyon baya masana'antun kasar da su rika martaba dokokin kasuwanci, a yayin da suke samar da muhimman ababen more jama'a a kasar da inganta hadin gwiwa da kasar game da makamashi. Bugu da kari, Sin tana fatan inganta hadin gwiwa da kasar Mozambique a bangaren makamashi, don kara cimma burin samun moriyar juna.
A nasa bangare, shugaban Nyusi ya ce, kasar Mozambique tana fatan inganta hakikanin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin makamashi, da ma'adinai, da aikin gona da yawon shakatawa a karkashin inuwar hadin gwiwar bangarorin biyu ko dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC.(Bako)