in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An halaka a kalla mutane 6 a yankin kudu maso gabshin Najeriya
2016-06-03 09:40:26 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa,a kalla mutane 6 ne suka rasa rayukansu bayan wasu da ake zaton mahara ne sun kai hari kan wani kwale-kwalen tafi-da gidanka na soja a jihar Delta da ke kudu maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun sojojin kasar Kyaftin Jonah Unuakhalu ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa, wata kungiyar masu dauke da makamai ne ta kaiwa kwale-kwalen kamfanin samar da mai na kasa NNPC da ke aikin sintirin duba bututan mai a mahadar Ejere da ke karamar hukumar Warri ta kudu hari, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji guda biyu,soja daya ya jikkata,daya kuma ya bace, yayin da aka harbe wasu ma'aikata fararen hula 4 da ke aiki da kwale-kwalen har lahira.

Jonah ya kara da cewa, maharan sun badda kama ne a matsayin fasinjoji, inda suka kaddamar da harin daga cikin wasu kwale-kwale masu dan Karen gudu.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China