A yanzu haka an bude cibiyoyin yin rijista kimanin 3,500 domin yin rijistar har na tsawon kwanaki 10 ga al'ummar Ghana 'yan shekaru 18 zuwa sama, domin su samu damar kada kuri'unsu a babban zaben kasar dake tafe.
Sai dai hukumar zaben kasar ta gargadi jama'a da su guji yin rjistar fiye da sau daya, kasancewar na'ura zata iya gano masu wannan yunkuri.
Za'a kammala aikin rijistar ne a ranar 8 ga watan Mayu, kuma za'a gudanar da babban zaben kasar a watan Nuwambar bana.(Ahmad Fagam)