in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana zata habaka fannin lantarki a kasar
2016-04-22 10:29:48 cri
Gwamnatin Ghana ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen wadata kasar da hasken wutar lantarki.

Mataimakin shugaban kasar Kwesi Bekoe Amissah-Arthur ya sanar da hakan a ranar Laraba a lokacin da ya kai ziyara wajen aikin samar da lantarki mai karfin mega watts 350 wanda kamfanin Cenpower ke gudanar, wani kamfani samar da lantarki ne mai zaman kansa, wanda kuma ke gudanar da aikin a Kpone, kusa da Tema, dake da tazarar kilomita 38 daga babban birnin kasar.

Ya ce gwamnatin kasar a shirye take ta goyi bayan duk wani shiri da ya shafi zuba jari a fannin lantarkin kasar, domin tabbatar da samun bunkasuwa ga sha'anin tattalin arzikin kasar.

Aiki wanda zai lashe tsabar kudi har dala miliyan 900 wanda cibiyar cigaban al'amurran kudi ta kasa da kasa DFIs tare da hadin gwiwar bankin Rand Merchant Bank kasar na Afrika ta kudu zasu samar da kudadaden aiki, kuma ana sa ran kammala aikin nan da shekarar 2017.

Amissah-Arthur ya yi alkawarin cewa, gwamnatin kasar za ta tabbatar da ganin an samu ingantaciyyar wutar lantarki domin kaucewa irin abin da ya samu kasar na katsewar lantarki a shekarun baya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China