Ministan tsaron Cote d'Ivoire Alain Donwahi, a yayin ganawar aiki ya ce, mu kasashe ne 'yan uwan juna dake makwabtaka. Muna raba damuwa guda ta fuskar tsaro kuma yana da fa'ida mu gamu domin yaki da dukkan bala'un dake kawo illa ga yanayin tsaron mu.
A cewarsa mista Donwahi, bukatar tsaron hadin gwiwa da musanyar kwarewa tsakanin kasashen biyu nada muhimmancin gaske.
A nasa bangare, ministan kasa na Guinee dake fadar shugaban kasa mai kula da harkokin tsaro Mohamed Diane ya nuna cewa an samu sakamako mai alfamu da makoma mai haske game da musanyar kwarewa a fannin gyare gyaren rundunar sojojin kasashen biyu.
A cewarsa, hadin gwiwar ayyuka zai taimaka wajen jajircewa yadda ya kamata game da dabarun da za amfani da su wajen yaki da ta'addanci, domin tabbatar da zama lafiya da kulawa mai kyau kan iyaka tsakanin Cote d'Ivoire da Guinee. (Maman Ada)