in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire: An bude wani taron ministoci kan tsaro a yammacin Afrika
2016-05-28 12:16:00 cri
Ministocin dake kula da harkokin tsaro, diplomasiyya da kudi na kasashen kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) sun bude taro a ranar Jumma'a a birnin Abidjan domin tattauna batutuwan dake da nasaba da zaman lafiya da tsaro a shiyyar.

A yayin bude zaman taron, shugaban Cote d'Ivoire, Alassane Ouattara, kuma shugaban taron shugabanni da gwamnatocin UEMOA, ya bayyana jin dadi kan bude taron a cikin wani yanayi dake tattare da karuwar ayyukan ta'addanci a yankin kungiyar UEMOA, musammun ma hare haren ta'addanci da aka kai a kasashen Mali, Burkina Faso da Cote d'Ivoire.

Baya ga ta'addanci, fataucin miyagun kwayoyi, makamai da jama'a, kaifin kishin addani, fashin teku, halatta kudade, bala'un mulalli da kiwon lafiya da ma sauransu na kasancewa wani tushen babbar damuwa ga tsaron jama'a da dukiyoyinsu a shiyyar da ma zaman karko na kasashe mambobin kungiyar.

Alassane Ouattara ya bukaci taron da ya bullo da tabbatattun muradu da za a cimma da nargartattun ayyuka da za a koyar domin bunkasa matakin hadin gwiwa na baki daya, ma'ana dai karfafa shawarwari tsakanin kasashen kungiyar da fito da hanyoyin hadin gwiwa yadda ya kamata domin kiyaye zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a shiyyar.

Shugaban Senegal, Macky Sall, shugaban kwamitin manyan jami'ai kan aiwatar da shirin zaman lafiya da tsaro, ya jaddada a nasa bangare bukatar yin aiki, aikin gaggawa da nagarta gaban kalubalolin tsaro da kasashen shiyar suke fuskanta.

Haka kuma, ya jaddada wajabcin karfafa karfin sanya ido, nazari da yin rigakafi game da barazana ta yanzu da ta gaba a yankin UEMOA.

Mista Sall ya mai da hankali nan gaba wajen kafa wani tsarin sanya da rigakafi na UEMOA tare da yin kira wajen ganin fara aikin babbar tawagar zaman lafiya da tsaro, da ya kamata ta samu wani matsayi da kayayyaki da zasu bata damar gudanar da aikinta yadda ya kamata kan aiwatar da siyasar hadin gwiwa ta zaman lafiya da tsaro na UEMOA.

A yayin taron, ministocin zasu kimanta matsalar tsaro baki daya a yankin UEMOA tare da duba hanyoyi da matakan fuskatar lamarin yadda ya kamata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China