in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi alkawarin tallafawa Burkina Faso wajen yaki da ta'addanci
2016-03-19 11:47:37 cri

Wakilin musamman na babban magatakardar MDD a yammacin Afirka Mohammed Ibn Chambas, ya ce MDD a shirye take, ta tallafawa mahukuntan Burkina Faso wajen shawo kan kalubalen 'yan ta'adda.

Mr. Chambas ya yi wannan tsokaci ne yayin zantawar sa da 'yan jaridu a birnin Ouagadougou fadar mulkin kasar ta Burkina Faso, jim kadan bayan ganawar sa da shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore. Ya ce MDD ta tattauna game da manyan matakan wanzar da zaman lafiya a kasar, ciki hadda batun inganta tsaro.

Burkina Faso dai na cikin kasashen yammacin Afirka, wadanda ke fuskantar barazana daga masu da'awar jihadi, wadanda sau da dama kan kaddamar da hare-hare kan ofisoshin 'yan sanda, a yankunan dake arewacin kasar. Ko da ma a ranar 15 ga watan Janairun da ya gabata, sai da irin wadannan mayaka suka kai harin ta'addanci kan wani Otel dake birnin Ouagadougou, harin da kuma ya hallaka mutane 30.

A farkon wannan wata na Maris, babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya ziyarci kasar, inda ya jaddada goyon bayan sa ga mahukuntan ta, a kokarin su na yaki da 'yan ta'adda.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China