Jam'iyyun APMP suna goyon baya da ba da kwarin gwiwa ga gwamnatin kasar da ta cigaba da kawo sauye sauyen tattalin arziki, jama'a da siyasa domin cigaban kasar, in ji kakakin wannan kawance, Adama Kanazoe, wanda shi ma ya kasance shugaban kawancen matasa domin 'yanci da jamhuriyya (AJIR), a yayin wani taron manema labarai. Ya kuma jaddada cewa APMP, wani gungun jam'iyyu da kungiyoyin siyasa ne dake goyon baya da kuma kare shirin siyasa na shugaba Kabore da kuma cigaban aiwatar da shi. (Maman Ada)