in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yabawa NLC bisa janye yajin aiki
2016-05-24 09:16:59 cri
Ministan watsa labarai na tarayyar Najeriya Lai Mohammed, ya jinjinawa kungiyar 'yan kwadago ta Najeriya NLC, bisa amincewa ta janye yajin aikin da ta shafe kwanaki 5 tana gudanarwa, sakamakon janye tallafin mai da gwamnatin kasar ta yi.

Ministan wanda ya bayyana hakan, yayin taron zantawa da jam'iyyun gama kai da ya gudana jiya Litinin a jihar Legas, ya ce matakin janye yajin aikin na da matukar fa'ida ga 'yan kasar.

Daga nan sai ya jaddada aniyar gwamnatin kasar mai ci, na cika alkawuran da ta daukarwa 'yan kasar, yayin da a hannu guda kuma, za ta rika tattaunawa da 'yan kasar da nufin jin ta bakin su game da hakan. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China