in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-05-23 19:14:29 cri
Wasu da ake zaton 'yan tawaye ne sun kai hari tare da cinna wuta a batutun mai na kamfanin mai na Agip a Ikienghenbiri da ke karamar hukumar kudancin Ijaw na jihar Bayelsa. Bugu da kari, 'yan tawayen sun kai wani hari kan bututun mai na kamfanin man Najeriya(NNPC) mai tsawon kilomita 5, kuma shi ne layin da ke samar da mai ga Machinver Jetty da ke jihar Cross Rivers(.The Guardina)

A jiya Lahadi ne babbar kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta dakatar da yajin aikin da yi niyyar shiga a duk fadin kasar a ranar Larabar da ta gabata, domin nuna adawa da karin farashin kudin mai da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi. Wata sanarwar da gwamnatin Najeriya ta fitar a daren jiya,ta yi maraba da shawarar kungiyar kwadagon na dakatar da shiga yajin aikin, inda ta bayyana kudurinta na hawa teburin sulhu da 'yayan kungiyar.(Daily Trust)

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta girke jami'anta a hedkwatar jam'iyyar PDP da ke Abuja,fadar mulkin kasar. Rundunar 'yan sandan ta dauki wannan mataki ne a jiya,don hana barkewar duk wani tashin hankali a sakatariyar jam'iyyar.( The Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China