in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron shekara shekara karo na 55 na kungiyar AALCC a Birnin New Delhi
2016-05-19 19:09:36 cri
An bude taron shekara shekara karo na 55 na kungiyar shawarwari game da dokoki tsakanin Asiya da Afirka ko (AALCC), a Birnin New Delhi fadar mulkin kasar Indiya.

Taron wanda zai guda tsakanin ranekun 17 zuwa 20 ga watan nan ya samu halartar manyan baki daga sassan biyu. Cikin jawabin da ya gabatar a ranar Talata 17 ga watan nan a yayin bikin bude taron, mataimakin ministan harkokin waje na Sin Liu Zhenmin, ya bayyana cewa a cikin shekaru 60 da kafuwar AALCC, kungiyar ta taka rawar gani a fannonin sa kaimi ga inganta mu'amala tsakanin kasashen Asiya da na nahiyar Afirka a fannin dokokin kasa da kasa, da kiyaye moriyar juna, da kuma bunkasa dokokin kasa da kasa.

Tuni dai tawagar Sin ta yi shawarwari da sauran tawagogin dake halartar taron kan dokokin kasa da kasa game da yanar gizo, da dokar yankin teku, da yaki da tsattsauran ra'ayi, da batun aikin kwamitin dokokin kasa da kasa da dai sauransu.

An kafa kungiyar AALCC ne a shekarar 1956, bisa kudurin taron Bandung, kungiyar da ta zama daya tak da ke tsakanin gwamnatocin kasashen nahiyoyin Asiya da Afirka dake bunkasa fannin dokokin kasa da kasa. Kawo yanzu akwai kasashe mambobin ta 47, da kasashe masu sa ido 2. Kaza lika Sin ce ta shugabanci kungiyar a karon da ya gabata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China