A ranar Talata ce shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya sanya hannu kan wata sabuwar doka, inda ya nada Ahmat Jidoud a matsayin ministan kasafin kudi.
Shugaba Issoufou ya kuma nada wani tsohon jagoran 'yan tawaye Rissa Ag Boula a matsayin minista a ofishin shugaban kasa, yayin da ya nada Chika Rakiato Bako mukamin minista mai kula da raya yankunan karkaka.
Brigi Rafini ne ke rike da mukamin firaministan gwamnatin Nijar din mai ministoci 41, 7 daga cikinsu kuma mata ne. (Ibrahim Yaya)