in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Nijar kusan ishirin ne suka mutu a yayin turmutsitsin Makka
2015-09-27 10:05:21 cri
A jimilce 'yan kasar Nijar 19 ne aka tabbatar a halin yanzu sun mutu a sakamakon turmutsitsin da ya faru a ranar Alhamis a Mina, dake kusa da birnin Makka a kasar Saudiyya, kuma har yanzu ba a da duriyarsu wasu karin mutane 50, a cewar wata sanarwar wucin gadi da babbar kungiyar dake kula da aikin hajji da ummara (COHO) ta kasar Nijar ta fitar a ranar Jumma'a.

A cewar wannan majiya, wasu 'yan Nijar tara kuma sun samu rauni a yayin wannan bala'in.

Aikin tantance gwawwaki na ci gaba da gudana tare da taimakon jami'an diplomasiyya na kasar Nijar dake Saudiyya, in ji malam Kady Abdoulaye, shugaban kungiyar COHO. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China