in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar/Harakar jarirai da aka sayo: soke shari'ar da ke tabbatar da ikon kotun hukunta laifuka
2016-03-25 11:00:27 cri
Bisa wani matakin da aka fitar a ranar Laraba, kotun daukaka kara ta birnin Yamai ta karya matakin kotu na ranar 13 ga watan Julin da ya gabata na tabbatar da ikon alkali na gudanar da shari'ar harkar sayo jarirai da gabatar da wannan harakar gaban kotu.

A shekarar 2014, akalin kotun Yamai ya bayyana cewa ba ya da kwarewar shari'ar harakar fataucin jarirai daga Najeriya, wani lamari ga mutanen da wannan harakar ta shafa na a yi watsi da tuhumar da aka masu.

A cewar Mossi Boubacar, lauyan da yana cikin mutanen da ake tuhuma wato Hama Amadou tsofon shugaban majalisar dokokin Nijar kuma abokin takarar da ya sha kasa na shugaba Mahamdou Issoufou a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa na ranar Lahadi 20 ga watan da ya gabata, abin da ya tilasta wannan mataki shi ne shari'ar akalin farko da ya bayyana rashin cancantarsa.

Shari'ar ta shafi kusan mutane talatin, Hama Amadou da matarsa, tsohon ministan kasa Abdou Labo da matarsa, laftana kanal Oumarou Tawaye da wasu sauran muhimman matune.

Mista Hama Amadou, da ya tsere kasar Faransa a ranar 27 ga watan Augustan da ya gabata, an cafke sa bayan ya dawo Nijar a ranar 14 ga watan Nuwamban da ya gabata tare da tusa keyarsa a gidan yarin Filingue mai tazarar kilomita 180 daga arewacin Yamai. A makon da ya gabata aka dauke shi zuwa kasar Faransa bisa dalilai na rashin lafiya.

Hama Amadou, babban mai adawa da shugaban kasa Mahamdou Issoufou, ya bayyana cewa tuhumar da aka masa ta siyasa ce, masu mulki a Nijar suna neman kauce sa daga zaben shugaban kasa na shekarar 2016. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China