in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar: Sojoji 6 sun mutu a wani harin Boko Haram a jihar Diffa
2016-01-17 16:47:57 cri
A kalla jami'an tsaro shida na rundunar sojojin Nijar ta FDS suka mutu yayin da biyar suka ji rauni, a ranar Asabar a wani aikin ta'addanci na mayakan kungiyar Boko Haram a Kablewa, dake gundumar Bosso, a jihar Diffa dake kuriyar arewa maso gabashin Nijar dake kusa da tarayyar Najeriya, a cewar wasu majiyoyi masu tushe dake birnin Niamey a ranar Asabar. A cewar gidan rediyo Anfani dake birnin Niamey, da ya rawaito wannan rahoto a cikin labarinsa na ranar Asabar da yamma, da kuma wasu majiyoyin soja suka tabbatar a wurin, ya bayyana cewa dakarun FDS sun ci karo da ajilinsu a lokacin da motar suke ciki ta taka nakiya a lokacin da suke gudanar da sintiri a wannan yanki inda mayakan kungiyar Boko Haram suke kai hare hare jehi jehi. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China