in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jinjinawa Togo game da tabbatar da adalci kan batun kudancin tekun Sin
2016-05-18 19:19:20 cri
A yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin Hong Lei, ya bayyana cewa kasar Togo, ta yi kira ga bangarorin da batun tekun kudu na Sin ya shafa da su yi biyayya ga yarjejeniyar dokokin teku ta MDD ko(UNCLOS)da sauran makamantan ta, matakin da kasar Sin ta jinjinawa Togo a kan sa, duba da cewa hakan ya kiyaye adalci kan wannan batu.

A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, wani dan jarida ya gabatar da tambaya game da labarin da ke cewa, ma'aikatar kula da harkokin waje da hadin gwiwa da ma dunkulewar kasashen Afirka ta Togo, ta gabatar da rahoto kan yanayin da ake ciki a tekun kudu na Sin. Yana mai bukatar karin haske game da ra'ayin kasar Sin game da batun.

Game da hakan ne kuma Hong Lei ya bayyana cewa, an riga an maida hankali matuka kan wannan rahoto na kasar Togo, bisa yadda kasar ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi biyayya ga jimla ta 298 ta yarjejeniyar UNCLOS da makamantan ta, a kokarin daidaita matsaloli ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.

Mr. Hong Lei ya kara da cewa, matsayin da kasar Togo ta dauka ya dace da hakikanin yanayin da ake ciki a tekun kudu na Sin, tare da matsaya daya da Sin da sauran kasashen da abin ya shafa suka cimma, dangane da daidaita matsaloli ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, da kuma dokokin kasa da kasa, kana hakan ya bayyana ra'ayin kasa da kasa bisa adalci kan wannan batu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China