Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mr. Okorafor, ta ce bankin na CBN na binciken ne domin gano hakikakin gaskiyar wasu zarge zarge da ake yiwa wasu daga bankuna cinikayyar kasar. A cewar sa za a ci gaba da aiwatar da hakan a kai a kai, musamman ma kan hada hada da ta shafi bankunan dake da alamar tambaya.
Sanarwar ta kara da cewa kare martabar tsarin da Najeriya ke bi wajen gudanar da harkokin kudi na da matukar muhimmanci, don haka ya zama wajibi bankuna da masu hulda da su, su kaucewa amfani da bankunan wajen aiwatar da huldodi da suka sabawa doka.
Yanzu haka dai hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriyar kafar ungulu, na binciken wasu manyan manajojin bankin Fidelity, da Sterling da bankin Access, bisa zargin su da karya dokokin cinikayyar bankunan kasar, da hadin gwiwar tsohuwar ministar albarkatun mai ta kasar Diezani Alison-Madueke. (Saminu)