in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta tallafawa fararen hula 38,000 a yankin Darfur
2016-02-16 10:48:12 cri
MDD ta ce ta tallafawa fararen hula 38,000 da rikicin yankin Darfur na kasar Sudan ya raba da muhallansu, da kayayyakin abinci da na masarufi, domin rage musu radadin halin da suka fada.

Wata sanarwa daga ofishin tsare tsare na ayyukan jin kai karkashin hukumar MDD mai kula da ba da agaji, ta ce mafiya yawan mutanen da suka samu tallafin, mata ne da kuma yara kanana, wadanda tashe tashen hankula a yankin Jebel Marra ya raba da matsugunnan su. Baya ga abinci mai gina jiki ga yara, an kuma samarwa 'yan gudun hijirar tallafin ruwan sha, da tantuna, da magunguna da dai sauran su.

Sanarwar ta rawaito shugabar ofishin tsare tsare, na ayyukan jin kai na MDD a kasar Sudan Marta Ruedas, na kira da a samar da tallafi mai dorewa ga al'ummun da yaki ya daidaita a yankin na Darfur.

A daya bangaren kuma, MDD ta jaddada matukar bukatar da ake da ita, ta dakatar da musayar wuta a yankin na Darfur, tare da jan hankalin daukacin sassan da wannan batu ya shafa, da su baiwa ma'aikatan hukumomin kasa da kasa, damar isa wuraren da 'yan gudun hijira ke samun mafaka a tsakiyar yankin na Darfur. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China