Ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya bayyanawa 'yan jarida bayan shawarwarin cewa, ministocin harkokin wajen kasashen hudu, sun amince da yin kokari tare wajen tabbatar da yanayin tsagaita bude wuta, bayan bikin Ista na kirista mabiya darikar Orthodox. Don haka, a cewar sa bangarori daban daban sun cimma daidaito kan matakai da ya dace a dauka na cimma wannan buri. Wato batun rushe hukumomin soja a sassan abkuwar rikici, da kafa yanki maras hukumomin soja, da janye dukkan makamai bisa yarjejeniyar da aka cimma kafin hakan. Tare da hana atisayen soja a yankin da ake fuskantar rikici, da kara mu'amala a tsakanin bangarori daban daban da rikicin ya shafa, da tuntubar juna a sassan da rikici ke aukuwa.
Haka zalika kuma, Steinmeier ya amince da cewa, bangarorin ba su cimma daidaito kan batutuwan da suka shafi yunkurin siyasa da zaben kananan hukumomi da dai sauransu ba. (Zainab)