A wata sanarwar da Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar AU ta fitar da a yammacin ranar Talata, ta yi Allah wadai da harin wanda aka kaddamar a filin jirgin sama na Zaventem da kuma babbar tashar jirgin kasa na Brussels, harin wanda ya yi sanadiyyar kashe fararen hula wadanda ba su ji ba su gani ba, da kuma raunata mutane masu yawa.
Dlamini-Zuma ta gabatar da sakon ta'aziyyar AU ga gwamnati da al'ummar kasar Belgium, da iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da yin fatan samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka a yayin harin.
Sannan ta jaddada aniyar AU ta kyamar dukkan nau'in ta'addanci da tsattsauran ra'ayi. (Ahmad Fagam)