Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi kira ga ma'aikata da su kasance masu aiki tukuru, gabanin bikin ranar ma'aikata na duniya wato ranar 1 ga watan Mayu.
Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin ganawa da fitattun masana kimayi da masu bincike da ma'aikata da dalibai matasa a lokacin da ya ziyarci lardin Anhui, ya kuma bukaci jama'a da su kasance masu nuna gaskiya a lokacin da suke gudanar da ayyukansu a kokarin da suke na cimma burinsu na rayuwa da canja makomarsu.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a yau Jumma'a, shugaba Xi ya ce kamata ya yi al'umma baki daya ta yi kokarin yayata akidar aiki tukuru, sannan ta yi watsi da duk wasu tunani marasa fa'ida, kamar ci da gumin wasu,amfani da wata dama da sharholiya.(Ibrahim)