Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bukaci jami'an jam'iyya da na gwamnati da su tsara matakan da za su biya bukatun jama'a a kokarin da ake na ganin an warware kuncin da ake fuskanta cikin shirin gyare-gyare na kasar.
Xi wanda shi ne sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci lardin Anhui daga ranar 24-27 ga watan Afrilu a kan yadda ake kaddamar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar daga shekara 2016-2020.
Xi ya ce, bisa la'akari da matsin lamba da sauye-sauyen tattalin arzkin ke fuskanta da karuwar batutuwan da suka shafi jin dadin jama'a, kamata ya yi a tabbatar cewa, an inganta rayuwar jama'a,kuma kamata ya yi shirin yin kwaskwarima ya fara da batutuwan da suka shafi jama'a kai tsaye.(Ibrahim)