Duk dai da sauye-sauyen da Getafe ke samu karkashin mai horas da wasan Juan Eduardo Esnaider, har yanzu kungiyar na fuskantar tarin kalubale, inda tuni ta kwashi rashin nasara har sau 11 cikin wasanni 13 da ta buga a baya bayan nan.
'Yan wasan Real Madrid karkashin kocin su Zinedine Zidane sun yi ta kokarin zura kwallaye a ragar, amma sai da aka kai ga mintuna 5 kafin tafiya hutun rabin lokaci ne Benzema ya jefa kwallon farko a ragar Getafe. Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne kuma kwallayen Madrid suka karu zuwa biyar, yayin da Getafe ta ci kwallo daya tak. Haka kuma aka tashi wasan Real Madrid na da kwallo 5 Getafe na da 1.(Saminu Alhassan)