Burkina Faso: An sako 'yar kasar Australiya Jocelyn Elliot da kungiyar AQMI ta sace a tsakiyar watan Janairu
Jocelyn Elliot, matar likitan nan dan kasar Australiya Ken Elliot, da su biyun kungiyar kishin islama Al-Qaida a reshen Magreb ( AQMI) ta sace a ranar 15 ga watan Janairu a arewacin kasar Burkina Faso, an sake ta a ranar Asabar da yamma, jim kadan bayan amsa alhakin wannan awon gaba, a cewar wata majiyar tsaro. Wannan majiya ta tabbatar da cewa tsofuwar wanda aka yi garkuwan da ita din ina zaton cewa tana karkashin kulawar hukumomin Nijar.
A cikin wani sakon rediyo, a ranar Asabar, kungiyar Al-Mourabitoune, dake tare da kungiyar AQMI a yankin Magreb, ta yi shelar sace wadannan ma'auratan biyu 'yan kasar Australiya, a ranar 15 ga watan Janairun da ya gabata a yankin arewacin Burkina Faso, a ranar da kuma da aka kai harin Ouagadougou, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan talatin. (Maman Ada)