Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da sakataren harkokin waje na kasar Japan Kisida Fumio wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Sin a yau Asabar a masaukin baki na Diaoyutai dake nan birnin Beijing.
Mista Wang ya bayyana cewa, kasashen Sin da Japan suna makwabta da juna, kuma kasar Sin tana fatan raya huldar sada zumunta tare da kasar Japan.
A sa'i daya kuma, Mr. Wang Yi ya bayyana bukatar raya wannan hulda bisa tushen girmama tarihi da cika alkawarran juna da kuma yin hadin gwiwa a maimakon nuna adawa ga juna. Yace Sin tana fata ziyarar Kisida za ta taka rawa mai yakini ga kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu.(Lami)