in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sanar da jadawalin bukukuwan tunawa da nasarar yakin kin harin Japan
2015-06-23 15:31:27 cri

A yau ne gwamnatin Sin ta fitar jadawalin jerin bukukuwan cika shekaru 70 da nasarar yakin kin harin Japan da jama'ar Sin ta yi da kuma nasarar yaki da masu ra'ayin Fascist na duniya.

A ranar 3 ga watan Satumba ne, za a shirya wani gagarumin bikin tunawa da wannan rana da kuma duba faretin rundunar soja a filin Tian'anmen bisa jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin da majalisar gudanarwa da kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa da kuma kwamitin tsakiya na rundunar soja na kasar Sin. Shugaba Xi Jinping zai halarci bikin tare da yin muhimmin jawabi.

Bugu da kari a wannan rana, za a shirya liyafa da bikin nuna wasanni a birnin Beijing. Kazalika, za a yi bikin ba da lambobin yabo don tunawa da cika shekaru 70 da nasarar yakin kin harin Japan ga tsoffin sojoji da jami'ai da suka taka rawar gani a yakin, lambobin yabon da shugaba Xi Jinping zai mika gare su.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China