in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yaba da sabunta wa'adin aikin tawagar UNOCI
2016-04-29 09:50:45 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi na'am da matakin da kwamitin tsaron MDD ya dauka, na tsawaita wa'adin aikin tawagar MDD dake aiki a kasar Cote d'Ivoire ko (UNOCI) a takaice, ya zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2017.

Cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, Mr. Ban ya ce hakan ya dace da irin nasarorin da aka cimma a kasar, ciki hadda kammalar babban zaben kasar na bara, matakin da ya baiwa tawagar MDDr zarafin shiga zango na karshe, na aikin wanzar da zaman lafiya da tawagar ta ke aiwatarwa a kasar.

Tuni dai kwamitin na tsaro ya umarci ofishin MDD da ya tabbatar da kammala janye daukacin dakarun sa masu kayan sarki, da ma jami'ai fararen hula, nan da karshen watan Afirilun shekarar ta 2017.

A wani ci gaban kuma, kwamitin tsaron MDDr ya amince da dage takunkumin hana sayen makamai, da na tafiye tafiye, da na daskaras da kadarori ga jami'an gwamnatin Cote d'Ivoire.

Mambobin kwamitin tsaron dai sun amince da hakan ne bayan gamsuwar da suka nuna, ga irin ci gaban da aka samu wajen daidaituwar lamurran gudanarwa a kasar. Cote d'Ivoire dai ta sha fama da tashe-tashen hankula bayan babban zaben shekarar 2010, lokacin da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, ya ki amincewa ya mika mulki ga zababben shugaban kasar Alassane Ouattara. Sai cikin watan Afirilun shekarar 2011 ne aka tursasa shi mika mulkin ga Mr.Ouattara.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China