Shugabar hukumar zaben kasar Charlotte Osei ita ce ta tabbatar da hakan bayan wani bore da ya barke a ranar Alhamis data gabata a Kumasi, birni na biyu mafi girma a kasar wanda ke da tazarar kilomita 270 a arewacin babban birnin kasar.
Wasu kafafen yada labarum kasar sun rawaito cewar, gungun magoya bayan jam'iyyun adawa ne suka shirya zanga zangar, inka suka nemi a samar da ingantaccen katin zabe ga masu kada kuri'u a babban zaben kasar wanda za'a gudanar cikin wannan shekara.
Shugabar hukumar zaben ta ce, tuni hukumar da dukufa wajen aiwatar da wasu sauye sauye, wanda kotun kolin kasar ta amince da su, don samun zabe mai inganci da za'a gudanar a ranar 7 ga watan Nuwanba, sabanin 7 ga watan Disamba kamar yadda aka ambata lokutan baya.