in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana ta sake inganta matakanta na tsaro
2016-03-17 13:28:48 cri
Gwamnatin kasar Ghana ta sake inganta matakanta na tsaro, bayan hare-haren ta'addancin da suka rutsa da kasashen Mali, Burkina Faso da Cote d'Ivoire.

Wata sanarwa da mahukuntan kasar suka futar a jiya Laraba, ta bayyana cewa, majalisar tsaron kasar ta yi bitar hare-haren baya-bayan da suka auku a wadannan kasashe da kuma harkokin leken asiri da ake gudanar game da ayyukan ta'addanci a yammacin Afirka.

Bugu da kari, majalisar tsaron kasar ta Ghana ta sake bitar shirin kota-kwana game da yaki da ta'addanci na kasar, ayyukan dakarun hadin gwiwa da sauran matakai da nufin tabbatar da tsaro a kasar.

Don haka, majalisar tsaron kasar ta shawarci jama'a da su rika sanya ido tare da yin taka tsan-tsan, sannan su rika kai rahoton duk wasu abubuwan da ba su amince da su ba ga hukumomin tsaro.

A ranar Talata ce shugaba John Dramani Mahama na Ghana ya jagoranci taron majalisar tsaron kasar da nufin bibiyar yanayin harkokin tsaron kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China