in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mu leka wurin tunawa da Kwame Nkrumah a kasar Ghana 
2016-04-18 16:11:12 cri

A birnin Accra na kasar Ghana, akwai wani wuri mai suna Kwame Nkrumah Memorial Park, wato wurin tunawa da marigayi Kwame Nkrumah, wanda shi ne shugaban kasar Ghana na farko a cikin tarihi. An haifi Kwame Nkrumah a shekara ta 1909, kuma ya rasu a shekara ta 1972. A duk tsawon rayuwarsa, yayi gwagwarmayar samun 'yancin kan kasar Ghana. Sakamakon kokarin da yayi, Ghana ta samu 'yancin kai a ranar 6 ga watan Maris na shekara ta 1957.

Shi Kwame Nkrumah tsohon aminin kasa Sin ne, wanda ya taba ziyartar kasar Sin sau biyu a shekara ta 1961 da 1966. A dakin tunawa da Kwame Nkrumah, akwai wasu hotunan da suka nuna zumuncin dake tsakanin Kwame Nkrumah da wasu tsoffin shugabannin kasar Sin.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China