160421-tsohon-dan-wasan-nba-marbury-ya-samu-izinin-zama-na-dindindin-a-kasar-sin-bello.m4a
|
Shahararren dan wasan Kwando na kasar Amurka, wanda ya taba wasa karkashin tsarin gasar wasan kwallon kwando na NBA, Stephon Marbury, ya samu izinin zama a kasar Sin na dindindin, inda ya nuna hoton takardar shaidar izinin zaman ta sa a shafin sada zumunta na Weibo a ranar Litinin.
Ban da haka kuma Marbury ya nuna hoton bidiyon da ya dauka, wanda ya sheda yadda ya karbi takardar shaidar izinin zaman, daga hannun Zhang Jiandong, mataimakin magajin birnin Beijing.
Da hakan Marbury, wanda ya kasance dan wasan bayan kungiyar kwallon kwando ta birnin Beijing, ya zama dan wasan kasar waje na farko da ya samu takardar shaidar izinin zama na dindindin a kasar Sin, tun bayan da aka kafa tsarin gasar wasan kwallon kwando ta kasar Sin CBA shekaru 21 da suka wuce.
Takardar shaidar izinin zama na dindindin wato 'green card' na da wuyar samu, ganin yadda tun bayan da aka fara samar da takardar a shekarar 2004, baki 'yan kasashen waje kimanin 5000 ne kadai suka samu mallakar ta, duk da cewa a yanzu a kasar Sin akwai 'yan kasashen waje kimanin duba 600. (Bello Wang)