in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 61 sun rasu a sakamakon hadarin jirgin sama a kasar Rasha
2016-03-19 13:01:03 cri

Wani jirgin sama dauke da fasinjoji da ya tashi daga birnin Dubai na UAE zuwa Rostov-on-Don dake kudancin kasar Rasha, ya fadi yayin da yake yunkurin sauka a filin jirgin kasar da sanyin safiyar yau, nan take kuma daukacin fasinjoji da ma'aikatan jirgin a kalla su 61 suka rasa rayukan su.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Rasha ya fitar, an ce yanayi maras kyau ne haddasa hadarin jirgin, kana dukkanin fasinjoji dake cikin sa 'yan kasar Rasha ne. Kaza lika an rawaito ma'aikatar lura da zirga-zirgar jiragen saman kasar ta Rasha na bayyana cewa, an ji karar wata fashewa yayin da jirgin saman ya fadi.

Yanzu haka dai, ba a tababar yawan mutanen dake cikin jirgin ba, kasancewar ma'aikatar kula da zirga-zirgar jiragen kasar ta bayyana cewa, yawan mutanen dake cikin jirgin sun kai 62, wadanda suka hada da fasinjoji 55 da ma'aikata 7. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China