Haka kuma, wakilin kwamitin ya bayyana a yayin wannan taro cewa, bisa kididdigar da aka yi, masu jefa kuri'u sama da miliyan 5 ne suka kada kuri'u a zaben, daga cikin mutane miliyan 8.8 da suka yi rijista a kasar, lamarin da ya sa masu jefa kuri'u suka kai kashe 57.56 cikin 100. Amma ba a gabatar da jam'iyyoyin da wadanda suka lashe zaben ba.
An gudanar da zaben majalisar dokokin Syria ne a ranar 13 ga wannan wata da muke ciki, kimanin 'yan takara 3000 suka fafata don neman kujeru 250 a majalisar dokokin kasar.
Bugu da kari, bisa tsarin mulkin kasa ta Syria, ana gudanar da zaben majalisar dokokin kasar ne bayan shekaru hudu, an gudanar da zaben majalisar dokokin kasar da ya gabata a ranar 7 ga watan Mayun shekarar 2012, inda jam'iyyar Arab Socialist Renaissance ta samu galibin kujeru majalisar.
Sabo da haka, ana ganin cewa mai yiwuwa ne jam'iyyar za ta sake lashe zaben da aka gudanar a wannan karon. Sai dai manyan jam'iyyun adawa na gida da na ketare sun kauracewa shiga zaben na wannan karo.(Maryam)