in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba da gudanarwar taron neman sulhu kan batun Syria zagaye na biyu
2016-04-19 20:44:43 cri
Yayin taron shawarwarin neman sulhu kan batun rikicin siyasar kasar Syria zagaye na biyu da ya gudana, an tattauna kan batun yin garambawul kan gwamnatin kasar Syria, da gyara tsarin mulkin kasa, da sauran harkokin dake shafar sauyin siyasa a kasar.

Dangane da wannan lamari, kakakin ma'aikatar hakokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Talata 19 ga wata cewa, kasar Sin na maraba da gudanarwar shawarwarin neman sulhu, wadda MDD ta yi kira da a gudanar, haka kuma tana fatan za a iya kaiwa ga warware batutuwan dake shafar kasar ta Syria ta hanyoyin da za su dace da bukatu na bangarorin da abin ya shafa kuma yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China