An dage sanya hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya da ya kamata a yi a ranar Litinin tsakanin gwamnatin DRC-Congo da gungun 'yan tawayen M23, in ji kakakin gwamnatin kasar Uganda, Ofwono Opondo.
Bangarorin biyu sun kasa cimma wata yarjejeniya dalilin cewa, tawagar gwamnatin DRC-Congo ta bukaci karin lokaci domin duba wannan yarjejeniya kafin ta sanya hannu, in ji mista Opondo ba tare da ba da wani lokacin da za a rattaba hannun ba.
Dage sa hannu ya zo daidai da sanarwar da kungiyar M23 ta bayar kan matakinta na sanya hannu kan irin wannan yarjejeniya tare da gwamnatin DRC-Congo a ranar Litinin a Uganda, inda aka gudanar da jerin tattaunawa tun cikin watan Disamban da ya gabta.
A cikin wata sanarwa ta ranar Litinin, M23 ta bayyana cewa, za a shirya wani biki a wannan rana a Entebbe, wani birnin Uganda domin sanar da kawo karshen tawaye.
Gungun 'yan tawayen, da tawayensu ya fara tun cikin watan Afrilun shekarar 2012 ya amince da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya. Babban jagoran mayakan M23, Sultani Makenga da daruruwan mambobinsa sun rasa sansanoninsu a DRC, sun gudu zuwa kasar Uganda kafin su nemi a yi sulhu a makon da ya gabata. (Maman Ada)