in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan adawan Burundi sun bukaci a aiwatar da yarjejeniyar Arusha
2014-04-25 10:52:30 cri

Kungiyar 'yan adawar kasar Burundi ta yi kira ga masu ruwa da tsaki na yarjejeniyar Arusha domin tabbatar da zaman lafiya da sasanta 'yan kasar Burundi da suka hada da shugabannin kasashen Uganda, Afrika ta Kudu da Tanzaniya da su kara rubanya kokari wajen sanya ido kan cigaban da ake samu game da rikicin siyasa da kasar Burundi ke fuskanta.

A cikin wata wasika da aka aike wa wadannan kasashe uku a ranar Laraba, kawancen jam'iyyun adawa na UPO ya bayyana cewa, sanya hannunsu yana da muhimmancin gaske domin kaucewa kasar sake fadawa cikin wani sabon rikicin siyasa da na kabilu kamar a shekarun baya.

Muna fatan za ku aike da wata tawagar musammun cikin gajeren lokaci a kasar Burundi domin gudanar da shawarwari tare da dukkan bangarorin da wannan matsala ta shafa, ta yadda za a sanin halin da ake ciki a yanzu, da kuma gano inda gaskiya take, in ji Jacques Bigirimana, shugaban UPO a cikin wasikar da ya aike wa shugabannin wadannan kasashe uku. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China