Kwamitin sulhu na MDD, ya yi kiran da a cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Congo da 'yan tawayen M23, inda ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa, da su warware matsalolin da suka haddasa tashin hankali a gabashin kasar ta jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC).
Kwamitin ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis, cikin wata sanarwar shugaba, inda kwamitin ya ce, ya yi maraba da sanarwar da 'yan tawayen na M23 suka bayar na kawo karshen tayar da kayar bayan, matakin da gwamnatin kasar ta amince da shi da kawo karshen duk wata fitina tsakanin gwamnati da kungiyar ta M23.
Kwamitin sulhun ya ce, fadan da kungiyar ta M23 ta kwashe watanni 19 tana yi, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, ciki har da ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD, kana daruruwan fararen hula suka bar gidajensu.
Idan ba a manta ba, a ranar 5 ga watan Nuwamba ne, 'yan tawayen na M23 suka ayyana kawo karshen tayar da kayan bayan da suka kaddamar tun a watan Afrilun shekarar 2012 a kasar, kuma gwamnatin kasar ta Congo ta tabbatar da wannan ci gaba da aka samu.
A ranar Litinin ne ake sa ran sanya hannun kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin sassan biyu, amma sai aka dakatar, bayan da jami'an kasar ta Congo suka bukaci karin lokaci domin su nazarci bayanan. (Ibrahim)